<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Babu sunan da ya fi sunan Yesunmu.
 Shi ne wanda suka ƙi cikin fushinsu.
 Sunan Yesu ba mai fi, Allah ne ya shaida shi.

[V2]
 2) Babu daɗin da ya fi daɗin sunansa.
 Babu ceto, babu rai, sai a wurinsa.
 Sama, duniya, Lahira Suna yabon sunansa.

[V3]
 3) Babu girman da ya fi girman sunansa.
 Sarkin Sarakuna shi, Mai Shari'a kuwa.
 Iko duka nasa ne, shi kaɗai mai mulki ne.

[V4]
 4) Sunan Yesu, ba mai fi cikin duniya.
 Kan Ekklesiya ne shi, hasken Sama kuwa.
 Iko, girma, ɗaukaka nasa ne har abada</lyrics>
<title>Babu Sunan da Ya Fi Sunan Yesunmu LW96</title>
<hymn_number>96</hymn_number>
</song>